Mogadishu: Mayaƙan Al-Shabab Sun Kai Hare-Hare Babban Birnin Somalia

Hukumomi a Somalia sun ce da sanyin safiyar yau Laraba mayakan Al-Shabab sun kai hari wani ofishin ‘yan sanda da wurin binciken ababen hawa a Mogadishu babban birnin ƙasar.

Tun tsakar dare ake jin karar harbe-harbe babu kakkautawa a wasu sassan birnin.

Ministan tsaron cikin gida Abdullahi Nor ya wallafa a shafin sada zumunta cewa jami’an tsaro sun yi nasarar murƙushe masu tayar da ƙayar bayan masu alaƙa da kungiyar Al-Qaeda.

Babu rahoton wanda ya jikkata ko asarar rai. A makon da ya wuce mutum shida ne suka mutu lokacin da wani dan kunar-bakin-wake ya ta da bam din da ke jikinsa.

Maharin ya yi nufin tayar da bam ɗin a wata karamar mota da ke dauke da wakilan gwamnati a wurin da ake yin zaben ‘yan majalisu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here