Ambaliyar Ruwa: Mutane 18 Sun Rasa Rayukansu a Kasar Brazil

Ambaliyar ruwa da mamakon ruwan sama da ake tafkawa da zabtarewar kasa sun halaka mutum 18 a biranen Rio de Janeiro da Petropolis na kasar Brazil.

Masu aikin ceto sun duƙufa domin lalubo wadanda suka tsira. Wani mutum da ya kuɓuta ya ce sun gagara taimakon mutane.

“Mun kasa taimakon mutane, muna ji muna gani guguwa da ruwa mai karfin gaske suka yi awon gaba da gidajenmu da makofta, da kyar muka kuɓuta,” in ji shi.

A ɓangare guda, magajin birnin Petropolis ya ayyana dokar ta-baci, yayin da Shugaba Jair Bolsonaro da ke ziyarar aiki a Rasha ya ce ya shirya tallafin gaggawa ga wadanda lamarin ya shafa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here