Shari’ar da Ake da Abba Kyari ba Zata Dauki Wani Dogon Lokaci a Kotu ba – Marwa

 

Har yanzu dai ba’a kammala shari’ar da ake da Abba Kyari da hukumar NDLEA ba.

Shugaban hukumar NDLEA ya bayyana cewa shari’ar da ake da tsohon mataimakin kwamishinan dan sandan ba zata dau wani lokaci ba.

Ya bayyana haka ne yayin da aka yi hira da shi da gidan talabijin din channels.

Shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA), Muhammad Buba Marwa yace shari’ar da ake da tsohon mataimakin kwamishinan dan sanda, Abba Kyari ba zata dauki wani dogon lokaci a kotu ba.

Marwa wanda ya bayyana haka a wani shirin gidan talabijin na channels ranar juma’a, yace kama sauran jami’ai biyu da ake zargi da laifin ya nuna cewa za’a gaggauta hukunci kan lamarin.

“An riga an kama jami’ai biyu da ake zargi da laifin kuma an tura su kurkuku, kaga wannan yana nuni da cewa shari’ar Abba Kyari ba ata dau wani lokaci ba, “Marwa.

Ya kara da bayyana cewa hukumar NDLEA tana bada hadin kai sosai akan lamarin, inda yace hukumomin sun yarda dari bisa dari da shari’a.

Yayin amsa wata tambaya akan yadda ake zargin cewa akwai sa hannun wasu jami’an hukumar NDLEA a harkallar miyagun kwayoyi tare da Abba Kyari, Marwa ya bayyana cewa hukumar tana karfafa jami’anta kuma jajirtattu ne akan ayyukansu.

Ya kara da cewa akwai jami’ansu da yawa da suka samu lambobin yabo saboda kin amsar cin hanci kuma karamcin su yana cigaba da kawowa hukumar sakamako mai kyau.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here