Sojojin Najeriya Sun Lalata Haramtattun Wuraren Tace Man Fetur 30 a Jahohi  3

Dakarun sojan Najeriya sun lalata haramtattun wuraren tace man fetur 30, sannan suka kwashe sama da lita miliyan 12 na gas na ɗin ababen hawa a ayyukan da suka yi a jihohin Delta, da Rivers da Bayelsa.

Daraktan yada labarai na rundunar sojan, Manjo Janar Bernard Onyeuko, shi ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai ranar Alhamis a Abuja.

“Kamar yadda sanarwar tace, sojojin sun gano tare da lalata haramtattun wuraren tace mai 30, da tankunan ajiye 37, da tanda 31, da manyan jiragen ruwa na katako 12, da na’urorin sanyaya wuri biyu, da ramukan ajiya uku, da ganguna na ƙarfe,” a cewarsa.

“A dunkule, sojojin sun kwato litar mai miliyan 12, da tataccen litar gas 150,000, da lita 4,000 na danyen mai da aka sata, da motocin tanka uku, da motoci uku, da bututu 73, da babura biyu, da motar bas daya, da Toyota kirar Camry daya, da ƙirar Mercedes Benz daya.

“Bugu da kari, an kama wasu barayin manyan wayoyin wutar lantarki biyu da ke da alaka da lalatawa da kuma sata.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here