Jami’an China Sun Tabbatar da Cewa Babu Wanda ya Tsira da Ransa a Jirgin da ya yi hatsari

 

Jami’an China sun tabbatar da cewa babu wanda ya tsira da ransa sakamakon hatsarin jirgin saman fasinja a lardin Guangxi a ranar Litinin da ta gabata.

Jirgin Boeing 737 ya taso ne daga Kunming zuwa Guangzhou, tare da mutane 132 a lokacin da ya yi hatsari ya fada cikin daji mai tsaunika.

Jami’ai sun ce babu alamun abubuwan fashewa a wurin da hadarin ya auku.

Ba a gano na’urar nadar bayanan jirgin daga jirgin saman China Eastern Airlines ba.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here