Uganda ta Harba Bama-Bamai ta Sama Kan ‘Yan Tawaye a DR Congo

 

Kasar Uganda ta harba bama-bamai ta sama kan maboyar ‘yan tawayen ADF a DR Congo a wajen yankunan da ba sa cikin inda kasar tare da kwabciyarta jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo ke fada da ‘yan tawayen ba.

Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni ya cesai da Kasar Dr Kongo ta amince kafin aka kaddamar da hare-haren ranar 4 ga watan Nuwamba, tare da lalata babban sansaninsu.

Mista Museveni, wanda ya yada hotunan bidiyon hare-haren a shafinsa na Tuwita, ya ce ‘yan tawayen sun fice ne daga inda ake gwabza fada su, sakamakon matsa musu da dakarun kawancen kasashen biyu ke yi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here