Rahotanni daga garin Daura a yankin karamar hukumar mulki ta Zurmi a jihar Zamfara na nuna cewar wasu ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu tagwaye mata a jihar.

Bayanai sun nuna cewar an sace ‘Yan matan ne tare da yin garkuwa da su a yayin da suka fita zuwa kai dinkin bikinsu da za ai nan gaba kadan.

’Yan bindigar dai sun nemi a basu kudin fansa kafin su saki wadannan ‘Yan tagwaye. Wakilinmu ya kira lambar wayar kakakin rundunar ‘Yan sanda ta jihar Zamfara amma bata shiga.

The post ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu tagwaye a Zamfara appeared first on Daily Nigerian Hausa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here