Yan ISWAP Sun yi Garkuwa da ‘Ya’Yan Gidan Sarautar Askira Uba

 

Miyagun ‘yan ta’addan ISWAP sun yi garkuwa da ‘ya’yan gidan sarautar Askira Uba har maza uku kan hanyarsu ta zuwa Maiduguri.

‘Yan ta’addan sun sace Mohammed Askira da kannansa biyu, wadanda dukkansu kannai ne ga mai martaba Sarkin Askira Uba.

‘Yan ta’addan na cigaba da cin karensu babu babbaka yayin da miyagu masu kai musu bayanan sirri ke kara kaimi.

Borno – ‘Yan ta’addan Islamic State of West Africa Province, ISWAP, sun sace dattijo mai shekaru 50 mai suna Mohammed Askira, tare da ‘yan uwansa maza biyu daga gidan sarautar Askira Uba a jahar Borno.

PRNigeria ta tattaro cewa, an yi garkuwa da su ne yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Maiduguri, babban birnin jahar Borno bayan halartar wani taro a garin Askira Uba.

Majiyoyi sun sanar da cewa, dattijon mai shekaru 50 da ‘yan uwansa maza biyun da aka sace duk kannai ne ga Mai Martaba Sarkin Askira Uba.

A yayin da ‘yan ta’addan ISWAP suka tsananta garkuwa da mutane a yankin, jama’a sun dinga nuna damuwarsu kan yadda al’amuran masu kai bayanan sirri ga ‘yan ta’adda ke hauhawa.

Suna bayyana bayanin kaiwa da kawowar jami’an tsaro da sauran mutane ga kungiyoyin ‘yan ta’adda a yankin, PRNigeria ta wallafa.

A cikin kwanakin nan ne kungiyar ta’addancin mai tarin hatsarin gaske ta nada Wali Sani Shuwaram, mai shekaru 45 a matsayin sabon shugaban ISWAP a yankin tafkin Chadi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here