‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 6 a Jihar Ondo

Aƙalla mutum shida aka kashe a wani harin bindiga da aka kai unguwar Sabo kan hausawa da ke cikin gari a jihar Ondo, cikin daren Laraba.

‘Yan bindiga su kai wannan hari ne sa’o’i 72 bayan harin da aka kai wani coci a Owo, tare da kashe mutum 40.

An kuma jikkata mutane da dama.

Rahotanni na cewa ‘yan bindiga a kan babura ne suka farwa unguwar.

Kakakin ‘yan sanda a Jihar, Funmilayo Odunlami ta tabbatar da harin, sai dai tace barayi ne suka kai harin.

 

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here