Ina Tare da Tinubu Kuma Zan Mara ma sa Baya Wajen Cimma Nasara a Zaɓen 2023 – Shugaba Buhari

 

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya ce, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ne mutumin da ya fi dacewa da takarar shugabanci a Najeriya.

Tinubu ya samu tikitin takara a APC a zaɓen fitar da gwani da aka kammala jiya Laraba a Abuja.

Shugaban a wata sanarwa da kakakinsa ya fitar, Malam Garba Shehu, na cewa yana tare da Tinubu kuma zai mara ma sa baya wajen cimma nasara a zaɓen 2023.

Ya kuma ce Tinubu shi ne mutumin da zai kare da inganta tsarin dimukuradiya da suka gina kasar a kai.

Shugaban ya kuma bukaci ‘ya’yan jam’iyyar su hada kai wajen cimma nasara a zaɓen 2023.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here