Yan Bindiga Sun Kashe Mutane, ƙone Gidaje da Motoci a Zamfara

 

Rahotanni daga Jahar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya na cewa ƴan bindiga sun abka garin Kuryar Madaro da ke cikin ƙaramar hukumar Kauran Namoda inda suka kashe mutane da dama tare da ƙone motoci da gidaje.

Wasu mazauna yankin sun shaida wa BBC Hausa cewa maharan sun shiga garin ne da misalin ƙarfe 10:00 na dare inda suka shafe sa’o’i suna ta’asa a garin.

Wani mazaunin garin ya ce sun ƙirga gawar mutum 19 zuwa yanzu waɗanda ƴan bindigar suka kashe.

Sannan sun kwashi abinci a shagunan mutane da dabbobi.

Ya ce gida 13 maharan suka cinna wa wuta da motoci 16 da suka hada da na ƴan sanda.

Wasu hotuna daga mutanen yankin sun nuna yadda aka ƙone gidajen mutane da wasu shaguna da aka ajiye citta.

Ƴan sandan Zamfara sun tabbatar da harin, inda suka ce sun tura jami’ansu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here