DSS ta Ankarar da Sauran Hukumomin Tsaro Kan Cewa ‘Yan Boko Haram Sun Koma Dajin Kaduna Daga Sambisa

 

DSS ta bukaci hukumomin tsaro da su kara kaimi wajen sa ido da tattara bayanan sirri saboda shugabannin Boko Haram na yin kaura daga Dajin Sambisa zuwa Kudancin Kaduna.

An tattaro cewa ’yan ta’addan sun fara yin kaura daga dajin Sambisa da ke Jahar Borno ne zuwa dajin Rijana da ke Karamar Hukumar Chikun a Jahar Kaduna.

Rahoto ya nuna cewa babban kwamandan Boko Haram, Ibrahim, tare da tawagarsa na shirin komawa karkashin jagorancin Adamu Yunusu, wanda aka fi sani da Saddiqu.

Kaduna – Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta nemi hukumomin tsaro a Kaduna da su kasance cikin shirin ko ta kwana kan yiwuwar kai hare-hare, Sahara Reporters ta rawaito.

Ta bayyana cewa shugabanni da dakarun kungiyar ‘yan ta’adda na Boko Haram sun koma wani daji a Kudancin Kaduna daga Dajin Sambisa.

A cikin wata sanarwa da jaridar Peoples Gazette ta gani, an ce yan ta’addan sun kaura daga dajin Sambisa a jahar Borno zuwa dajin Rijana da ke karamar hukumar Chikun ta Kaduna.

Jaridar ta rawaito wani bangare na bayanin yana cewa:

“Wani babban mayakin Boko Haram, Ibrahim (FNU) tare da sojojinsa” suna ƙaura don komawa cikin takwarorinsu” karkashin jagorancin wani Adamu Yunusu (wanda ake kira Saddiqu)”.

Don haka, DSS, ta umarci jami’an tsaron Najeriya da jami’an NSCDC da su tsaurara tsaro a yankunan da aka ambata da kuma kewaye, inda ya kara da cewa yakamata ta sanya jami’an ta cikin shiri da bayar da rahoto yadda ya kamata.

A cewar jawabin, “an kuma umurce NSCDC da ta kara sa ido da tattara bayanan sirri a yankunan da aka ambata.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here