Abu Mai Fashewa ya Fashe a Yakin Rigasa da ke Jahar Kaduna

 

Mazauna yankin rigasa sun shiga ruɗani, yayin da wani abu mai fashewa ya fashe a daren Juma’a kusa da mai P.O.S, wajen wani masallaci.

Lamarin ya ritsa da mutane uku, wanda daga cikinsu mai P.O.S din ne yafi samun matsanancin rauni, daga bisani aka garzaya dashi asibiti.

Hakan ya faru ne, bayan wasu makonni da kwamishinan kula da lamurran cikin gida ya bukaci jama’a da su sa ido, duba da rahoton yadda ƴan ta’adda ke shirin dasa abubuwa masu fashewa a wurare.

Mazauna yankin Danmani na Rigasa, cikin ƙaramar hukumar Igabi dake jihar Kaduna sun shiga tashin hankali bayan fashewar wani abu a daren juma’a.

Lamarin ya auku ne, kusa da shagon P.O.S, wajen masallacin Abubakar Sadiq, kamar yadda mazauna yankin suka bayyana.

Daily Trust ta tattaro yadda aka ga wani abu mai fashewa kusa da wani babur, wanda ake tunanin mallakin mai shagon P.O.S din ne a yankin.

Wani ɗan sa kan yankin, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya labarta yadda fashewar abun ya raunata mai P.O.S din, wanda daga bisani aka garzaya dashi asibiti.

“An garzaya da mutumin asibiti don nema masa lafiya, saboda kafafunsa da ƙunbunan kafafun sun samu rauni matuka. Amma, an kai wa ƴan sanda kara,” a cewarsa.

Wani mazaunin yankin mai suna Shehu, ya bayyana yadda mutane uku suka samu raunuka yayin aukuwar lamarin.

A cewarsa, rundunar cire bam ta isa wurin, inda ta tsaida tashin wani abu mai fashewan.

“Daga cikin mutane ukun da suka samu raunukan, akwai mai P.O.S din wanda baya cikin hayyacin shi, sannan yana samun kulawa a asibitin 44, inda sauran mutane biyu suka samu kananan raunuka,” a cewarsa.

Sai dai, gwamnatin jihar da ƴan sandan jihar har yanzu ba su yi tsokaci game da lamarin ba. Kakakin rundunar, ASP Jalige Mohammed, bai amsa kiran wayar da aka yi masa ba.

Daily Trust ta ruwaito yadda fashewar abun yazo wasu makonni bayan gwamnatin jihar ta bakin kwamishinan kula da lamurran cikin gida, Samuel Aruwan, ta ja kunnen mazauna yankin da su zama masu sa ido, saboda ƴan ta’adda na shirin dasa abubuwa masu fashewa a makarantu, kasuwanni da wuraren bauta.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here