Rundunar ‘Yan Sandan Jahar Neja Sun Kama Mai Kai wa ‘Yan Bindiga Abinci

Rundunar ‘yan sandan Jihar Neja ta yi ram da wani Umar Dauda, mai shekaru 20 da ake zargin yana kai wa ‘yan ta’addan jihar kayan abinci.

An samu wannan bayanin ne ta wata takarda wacce kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Wasiu Abiodun ya sanya wa hannu.

A cewarsa, sun samu bayanan sirri ne a ranar 16 ga watan Maris din 2022 akan yadda ake ganin shige da ficen matashin da kayan abinci a kauyen Kapako da ke Lapai.

Neja – Rundunar ‘yan sandan Jihar Neja ta kama wani matashi mai shekaru 20, Umar Dauda wanda ake zargin yana kai wa ‘yan ta’adda kayan abinci a jihar, The Punch ta ruwaito.

A wata takarda wacce jami’in hulda da jama’an rundunar ‘yan sandan jihar, Wasiu Abiodun ya sanya wa hannu, an samu bayani akan yadda aka kama matashin bayan mazauna yankin sun bayar da bayanan sirri ga hukuma.

An samu kudi mai yawa a hannunshi

Kamar yadda takardar tazo:

“An yi kamen ne a ranar 16 ga watan Maris din 2022, da misalin karfe 11 na dare bayan samun bayanan sirri akan yadda ake yawan ganin wani mai kai wa ‘yan ta’adda kayan abinci a kauyen Kapako da ke Lapai.”

Abiodun ya ce an tura rundunar ‘yan sanda daga ofishin Lapai da wasu ‘Yan Sa Kai zuwa kauyen bayan kwashe sa’o’i ana kulawa da shige da ficensa. Daga nan suka kama shi.

Kakakin ya ce bayan bincike shi tas, an gano wasu kayan abinci da kudade a wurin shi.

The Punch ta nuna yadda ya ce:

“Bayan kama shi, an samu sinkin biredi 6, goruna 4 na wani lemu Fearless, gorunan Maltina 5, dauri 5 na wani ganye da ake zargin wiwi ne, wanke danye da shinkafa, sai kuma kudi N90,000,000.”

Ya amsa laifukansa

Ya ci gaba da shaida yadda wanda ake zargin ya amsa laifukansa na kai wa ‘yan bindiga kayan abinci, kuma suna bin shi har sansaninsa don amsar kayan abincin.

Ya kara da cewa, Dauda ya shaida cewa wannan ne karonsa na 4 na kai wa ‘yan bindigan kayan abinci kafin a kama shi.

Takardar ta ci gaba da shaida yadda aka duba gidansa inda aka ga wata bindigar toka kuma ya amsa da cewa nashi ne.

Ya ce ya siya bindigar ne a N65,000 a hannun wani mai hada bindigogi a kauyen, kuma yana ajiyeta ne don kare kansa.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here