An Kashe Mutane 3, da Kona Gidaje 15 a Jahar Imo

Aƙalla mutum uku suka mutu da kona gidaje 15, ciki harda fadar masarautar Aborshi na al’ummar Izombe da ke karamar hukumar Oguta a jahar Imo da ke kudancin Najeriya.

Shaidu sun daura alhaki kan sojoji da suka kai harin ramuwar gayya a cewar Jaridar Daily Trust ta Najeriya.

Rahotanni na cewa sojojin sun fusata ne bayan kisan abokan aikinsu biyu da ake zargin matasan Izombe da aikatawa.

Wani shaida ya sanar da cewa matasa na bore kan kisan wani matashi da aka bayyana sunansa da Chukwunoso Iherue, zanga-zangar ce ta kai ga hallaka sojojin biyu.

Kakakin sojin runduna ta 34, Capt Joseph Akubo, a lokacin da aka tuntube shi ya shaida cewa ba shi da cikakken masaniya kan abin da ya faru.

Sai dai ya alkawarta bada bayanai da zaran ya samu karin haske.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here