Yan Bindiga Sun Sake Sako Dalibai 5 na Makarantar Baptist Bethel

 

‘Yan bindiga a jahar Kaduna sun sake sako dalibai biyar na makarantar Baptist Bethel da ke Kaduna.

Rabaren Israel Adelani Akanji, ya tabbatar da sakin daliban 5 da aka yi tare da mai kula da su guda daya.

A watan Yuli, miyagun sun sace dalibai 121 daga makarantar da ke karamar hukumar Chikun ta jahar Kaduna.

Kaduna – Miyagun ‘yan bindiga sun sake sako karin dalibai biyar na makarantar Bethel Baptist da ke karamar hukumar Chikun ta jahar Kaduna.

Daily Trust ta rawaito cewa, Rabaren Israel Adelani Akanji, shugaban Nigerian Baptist Convention ya tabbatar da sakin daliban da aka yi a daren Juma’a.

“Godiya ta tabbata ga Ubangiji. Biyar daga cikin daliban makarantar Bethel Baptist da mai kula da su 1 an sako su da yammacin nan, 8 Oktoba.”

“Muna godiya ga Ubangiji kuma mun yarda cewa sauran daliban hudu za a sako su. Muna godiya da addu’o’in ku da goyon bayan ku,” takardar tace.

Miyagun da suka kai farmakin sun yi awon gaba da dalibai 121 daga dakunan kwanansu kuma suka bukaci N500,000 a matsayin kudin fansan kowanne dalibi.

Tun daga nan, ‘yan bindigan sun cigaba da sakin daliban kashi-kashi.

A kashin farko an sako dalibai 28 a ranar 25 Yuli bayan iyayensu sun biya wasu kudin da basu bayyana ba.

Biyu daga cikin daliban sun tsero daga hannun ‘yan bindigan yayin da suka sako daya sakamakon rashin lafiyan da ya ke fama da ita, Daily Trust ta rawaito.

A ranar 26 ga watan Yuli, 3 daga cikin daliban sun sake tserowa daga hannun wadanda suka sace su.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here