‘Yan Sakai Sun Kashe Mutane 10 da Limamin Masallaci a Jahar Sokoto

Yan sakai, waɗanda gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal, ya haramta sun kashe wani limami da wasu mutum 10.

Rahotanni sun bayyana cewa an kashe mutanen ne baki ɗayansu a kasuwa, yayin da wasu huɗu suka jikkata.

Wani ɗan uwan limamin da aka kashe, yace ba abinda ɗan uwansa ya yi sai kawai dan yakasance Bafullatani.

Sokoto -Wasu yan bindiga da ake tsammanin yan ƙungiyar sakai ne da aka haramta, sun hallaka mutum 11 a Sokoto, kamar yadda dailytrust ta rawaito.

Rahotanni sun bayyana cewa akwai limamin masallaci daga cikin mutanen da maharan suka kashe a ƙauyen Mamande, ƙaramar hukumae Gwadabawa.

Legit.ng Hausa ta gano cewa baki ɗaya mutanen sun mutu ne nan take, yayin da wasu mutum huɗu da suka jikkata aka kaisu asibiti domin duba lafiya.

Wane limami aka kashe?

Limamin da lamarin ya shafa, Malam Aliyu, an tabbatar da cewa shine yake jagorantar musulmai sallah a masallacin Salame.

Harin na yan sakai waɗanda aka fi sani da yan bijilanti a Sokoto, ya faru ne da misalin ƙarfe 3:30 na rana.

Rahoto ya nuna cewa baki ɗaya mutanen da aka kashe sun fito ne daga rugar fulani kala daban-daban, inda suka zo kasuwa siyan kayan abinci.

Yan sakai sun farmaki kasuwar ba zato babu tsammani, kuma suka sheƙe mutanen, waɗanda suke zargi da tallafawa yan bindiga.

Shin dagaske mutumin yana jagorantar sallah?

Ɗaya daga cikin yan uwan limamin, Abdullahi Riskuwa, yace an kashe ɗan uwansa ba tare da wata hujja ba domin bashi da wani kashin kaji a jikinsa.

Riskuwa yace:

“Yana da ilimin addinin musulunci kuma ya kasance yana limancin sallah a ɗaya daga cikin masallatan mu na garin Salame.”

“Laifinsa ɗaya ne, saboda ya kasance ɗan kabilar fulani ne. Amma ba abinda yakai Aliyu kasuwa sai don ya sayi kayayyaki.”

Wane mataki jami’an tsaro suka ɗauka?

Da aka tuntubi kakakin rundunar yan sanda reshen jahar Sokoto, ASP Sanusi Abubakar, yace ba shi da masaniya kan lamarin.

Gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya haramta ayyukan yan sakai a faɗin jahar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here