kudaden Paris Club: Kotu ta yi Watsi da Karar da Manyan Lauyoyin Gwamnatin Jahohi 36 Suka Shigar Kan Gwamnatin Tarayya

 

Abuja- Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da karar da manyan lauyoyin gwamnatin jihohi 36 suka shigar kan gwamnatin tarayya.

A cikin karar, jihohin na kalubalantar shirin cire dala miliyan 418 daga asusun tarayya don biyan basussukan da wasu masu ba da shawara na jihohi da kananan hukumomi ke bin su dangane da kudaden Paris Club.

Mai shari’a Inyang Ekwo ya yi watsi da karar ne a wani hukuncin da ya yanke a ranar Juma’a, yana mai cewa manyan lauyoyin ba su kawo isassun shaidun da za su ba su zamsar da kotu ba.

Kafar yada labarai ta Channels Tv ta ruwaito cewa, alkalin ya ce babu wata kwakkwarar hujja da ta nuna cewa gwamnonin jihohin 36 sun amince da shigar da karar.

A cewar alkalin, an samar da ofishin babban Lauyan Jiha ne a karkashin sashe na 195 na kundin tsarin mulkin kasar na 1999, sannan kuma AG na jiha gwamna ne ke nada shi, wanda hakan ya sa AG ya zama wanda ke aiki a karkashin ikon wani gwamna.

Ya ci gaba da cewa jayayyar da masu shigar da kara suka yi na cewa ba bangaren shari’a ba ne, bai kai ga ci ba, domin kungiyar gwamnonin Najeriya da kungiyar kananan hukumomi sun shiga cikin karar.

Kotun ta ci gaba da cewa wadanda suka shigar da karar sun amince da akwai bashin da ake bi, inda suka dage cewa shigar da karar wata dabara ce ta kalubalantar bashin da ake bi.

Mai shari’a Ekwo ya bayyana cewa matakin da masu shigar da karar suka dauka na nuna cin zarafin tsarin shari’a ne, inda daga bisani ya yi watsi da karar saboda rashin cancantarta.

Karin bayani na nan tafe…

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here