Bola Tinubu ya Bawa LASU Gudumawar Naira 1bn

Tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya ba da gudummawar Naira biliyan 1 don gina cibiyar jagoranci a jami’ar jihar ta Legas.

Mataimakin shugaban jami’ar ta jihar Legas ne ya sanar da bayar da gudummawar a lokacin taron yaye dalibai na jami’ar karo na 25.

Tinubu ya jagoranci al’amuran jihar Legas daga 1999 zuwa 2007 kuma tun daga nan ya zama shugaban jam’iyyar APC na kasa.

Dan takarar shugaban kasa kuma jigo a jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya baiwa jami’ar jihar Legas (LASU), gudunmawar kudi don gina wata cibiyar bunkasa ilimin jagoranci da ya kai Naira biliyan 1.

Mataimakin shugaban jami’ar LASU, Farfesa Ibiyemi Olatunji-Bello ne ya sanar da bayar da gudummawar a taron lacca yaye dalibai karo na 25 a ranar Alhamis, 24 ga watan Maris.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa, mataimakin gwamnan jihar Legas Dr. Obafemi Hamzat ne ya wakilci Tinubu a wajen taron.

Da yake magana ta bakin Hamzat, Tinubu ya bukaci gwamnati ta tallafa wa masana’antun dabaru da za su dauki matasa aiki tare da samar da ayyukan yi.

Ya ce tallafin da gwamnati ke bayarwa na kere-kere da masana’antu zai kara bude kofa ga fara sana’o’in da kasuwanci tsakanin matasa.

A fadinsa:

“Manufofin masana’antu da ayyukan yi na kasa dole ne su yi tashi daga shafukan takardu su zo cikin rayuwa ta zahiri.

“Wannan zai taimaka wajen gyara al’umma don inganta tattalin arzikin matasa a cikinta.

“Muna bukatar sabuwar hanya mai gamsarwa, hanyar da za ta ba ku dama mai kyau a kyakkyawar damar samun wadata mai dorewa.”

Wadanda suka halarci taron a jihar Legas

Wadanda suka halarci bikin sun hada da Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano, da wakilan gwamna Aminu Masari na jihar Katsina, da mataimakin gwamnan jihar Borno, da mataimakan shugabannin jami’o’i daban-daban na kasar nan.

Haka kuma, akwai tsoffin gwamnonin jihar Legas biyu, Gimbiya Adejoke Adefulire da Dr Idiat Adegbule, kamar yadda Independent ta ruwaito.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here