Mika Kyari ga Amurka: Kotu ta yi Watsi da Buƙatar Gwamnatin Najeriya

 

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, babban birnin Najeriya ta yi watsi da ƙarar da gwamnatin ƙasar ta shigar ta shigar ta neman a tasa ƙeyar Abba Kyari, mataimakin kwamishinan ɗan sandan da aka dakatar saboda zarginsa da karɓar cin hanci daga Ramon Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppi.

Mai shari’a Inyang Ekwo ya yi fatali da ƙarar da Ministan shari’a, Abubakar Malami, ya shigar bisa dalilin cewa ƙarar na da naƙasu.

A watan Yulin 2021 ne rundunar ‘yan sanda ta Najeriya ta dakatar da DCP Abba Kyari bisa zargin karɓar cin hanci daga Hushpuppi – mutumin da ke tsare a Amurka bisa zargin damfarar miliyoyin dala.

Kyari na cikin zaratan jami’an ‘yan sandan Najeriya da suka yi fice wajen yaki da miyagun laifuka a kasar, yayin da wannan batu na cin hanci da rashawa ya haifar da cece-kuce a sassan kasar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here