Kamfanin NNPC ya Gaza a Bangaren Kasuwancin Mai – El-Rufai

 

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai, ya ce gwamnatin tarayya ta gaza a bangaren mai da kuma iskar gas, inda ya ce ya kamata ta fice daga bangaren kasuwancin.

El-Rufai ya bayyana hakan ne yayin taron zuba jari da hukumar karfafa zuba jari ta jihar Kaduna ta shirya.

Gwamnan ya ce bangarori da ke aiki a wannan kasa kamar bangaren nishadi da harkar sadarwa da kuma fasaha da sauransu, gwamnati ba ta da hannu a cikinsu.

A cewarsa, babu wani abu da ya sauya tun bayan cefanar da babban kamfanin man fetur na Najeriya a watan Yulin 2022.

Ya kara da cewa duk da irin kokari da shugaban kamfanin na NNPC, Mele Kyari yake yi, kamfanin ta gaza a bangaren kasuwancin mai.

“NNPC babbar matsala ce ga Najeriya wacce ta fi karfin mutum daya wanda muddin ba a shawo kan matsalar ba, to za ta iya durkusar da Najeriya,” in ji El-Rufai.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here