ƙara Farashi: Hukumar PCACC ta Kama Manajojin Gidan Man Fetur 4 a Jahar Kano
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Jihar Kano a Najeriya (PCACC) ta kama manajojin gidajen man fetur huɗu saboda zargin su da sayar da man fiye da farashin da aka ƙayyade na N165 kan lita ɗaya.
Read Also:
Kazalika hukumar ta kama ma’aikatan gidajen mai biyu.
Muƙaddashin Shugaban PCACC Mahmoud Balarabe ya ce sun kama mutanen ne a gidajen mai daban-daban na jihar.
Ya ƙara da cewa sun samu ƙorafe-ƙorafe daga jama’ar gari cewa duk da ƙarancin man da ake fama da shi wasu gidajen mai na sayarwa kan N200 zuwa N208 a Kano.