An Saki Tsohon Mataimakin Gwamnan Nasarawa Bayan Garkuwa da Shi

 

Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sako tsohon mataimakin gwamnan jihar Nasarawa a Najeriya, Onje Gye-Wado, bayan sace shi da suka yi a ranar Juma’a.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Najeriya a jihar, Ramhan Nansel ne ya tabbatar da hakan ga manema labaru a ranar Litinin.

Nansel ya ce tsohon mataimakin gwamnan ya kwashe kwana biyu a hannun ƴan bindiga, waɗanda suka sako shi a cikin dare, ranar Lahadi, bayan matsi daga jami’an ƴansanda masu neman inda yake.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne dai wasu mahara suka yi awon-gaba da Gye-Wado bayan kutsawa cikin gidansa da ke ƙauyen Gwagi a jihar ta Nasarawa.

Inda daga baya jami’an tsaro suka ce sun bazama domin gano inda ake garkuwa da shi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here