Zaman Gidan Yari: Kotun Afrika ta Kudu ta yi Watsi da Soke Hukuncin da Aka Yanke wa Tsohon Shugaban Kasar, Jacob Zuma

 

Babbar kotun Afirka ta Kudu ta yi watsi da yunkurin tsohon shugaban kasar Jacob Zuma na neman a soke hukuncin zaman gidan yari na watanni goma sha biyar da aka yanke masa.

Dan shekaru saba’in da tara a duniya, ya shaida wa kotun cewa hukuncin ya wuce gona da iri, kuma gidan yarin zai jefa lafiyarsa cikin haɗari.

Mista Zuma – wanda ke asibiti yana murmurewabayan yi masa tiyata – an daure shi saboda kasa bayar da shaida a binciken cin hanci da rashawa.

Ya musanta aikata ba dai-dai ba.

Tsare shi da aka yi a watan Yuli ya haifar da tarzoma wadda ta yi sanadin mutuwar sama da mutane dari uku.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here