‘Yan kasuwa a Dubai Sun Fara Kuka da Kewar ‘Yan Najeriya

 

‘Yan Najeriya ne kaso 18% na masu siyayya a shagunan kayan alatu a Dubai, a cewar ‘yan kasuwan da suka shiga jimamin rashin ‘yan Najeriya.

Hana ‘yan Najeriya bizan shiga Dubai ya fara shafar kasuwancin masu shagunan kayan alatu a kasar ta Larabawa.

Idan baku manta ba, an shiga cece-kuce da jimamin yadda aka fara hana ‘yan Najeriya shiga Dubai saboda wasu dalilai.

Rashin ‘yan Najeriya a birnin Dubai ya jawo ‘yan kasuwa masu manyan shaguna sun fara kokawa da rashin cinikin kayan alatu.

Kwanakin baya ne kasar Dubai ta haramta bizanta ga ‘yan Najeriya saboda wasu dalilai da kasar bata bayyana su a hukumance ba.

Dubai dai na daya daga cikin kasashen da ‘yan Najeriya ke zuwa sharholiya da kashe kudadensu, musamman a lokutan bukukuwan kirsimeti.

Da yawan ‘yan Najeriya da ke zuwa Dubai sukan siya zinare da kayan karau gami da kayan sakawa, takalma da sauran kayayyakin amfani yau da kullum.

‘Yan kasuwa sun fara kuka da kewar ‘yan Najeriya

Wasu ‘yan kasuwa a kasar sun fara koka yadda suke ganin sanyin kasuwa, ga kuma ciniki ya ragu duk dai saboda rashin ‘yan Najeriya a kasar.

Rahoton BusinessDay ya bayyana cewa, ‘yan kasuwan da kansu suka ce a yanzu kasuwar bata ci saboda dama ‘yan Najeriya ne masu saye kayayyaki a kasar fiye da kima.

Don haka, ‘yan Najeriya na daga cikin wadanda za su bugi kirji suce sune silar kudaden shigan Dubai idan ana maganar kayan alatu.

Yadda aka hana ‘yan Najeriya shiga Dubai

Legit.ng ta tattaro cewa, a watan Satumban bana, kasar Dubai ta fara daina ba ‘yan Najeriya biza.Dukkan neman biza da aka yi tun watan Oktoba, sai dai a dawo dashi ba tare da bahasin amincewa ba duk kuwa da biyan kudin da ya kamata.

Ana haka ne hukumar kula da tafiye-tafiye ta DMCs ta sanar cewa, a yanzu ta daina ba ‘yan Najeriya biza.

Sai dai, babu wata sanarwa a hukumance da ta fito daga kasar Dubai, wacce ke cewa an hana ‘yan Najeriya shiga kasar.

A baya an ga yadda ‘yan Najeriya ke kukan yadda ake hana bizan shiga kasar Dubai, lamarin da ya jawo cece-kuce.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here