Boye N19.3bn: Gwamnatin Jahar Kogi ta Kai EFCC Kotu

 

Gwamnatin jahar Kogi ta je kotu a kan zargin EFCC na cewa ta boye wasu Naira biliyan 19.3 a banki.

Babban akawun jahar Kogi da wani kwamishina suka kai karar hukumar EFCC a wani kotu a jahar.

Lauyoyin jahar Kogi suna so Alkali ya tursasawa EFCC ta biya su N35bn saboda bata masu suna.

Kogi – Gwamnatin jahar Kogi ta shigar da karar EFCC a gaban kotu a kan zargin da tayi mata na cewa ta boye N19.3bn da ta karba daga gwamnatin tarayya.

Jaridar The Cable tace babban akawun jahar Kogi, Momoh Jibrin, da kwamishinan kudi da tattali, Asiwaju Mukadam Asiru, sun kai kara a babban kotun jahar.

Hukumar EFCC mai yaki da rashin gaskiya da wani banki da CBN ne wadanda za su kare kansu a wannan shari’a rda ta ke gaban Alkali mai shari’a J. Majebi.

Alkali ya fadawa EFCC ta yi hattara

Mai shari’a J. Majebi na babban kotun jahar Kogi, ya bada umarni ga EFCC ta daina wallafa wani bayani a game da wannan magana da yanzu ta na gaban kotu.

Alkali ya ja-kunnen EFCC a kan yin magana game da abin da ya shafi wannan banki da asusu mai lamba 0073572696 wanda gwamnatin jihar Kogi ta mallaka.

Gwamnatin jihar ta na bukatar a biya ta Naira biliyan 35 saboda bata mata suna da tace hukumar ta EFCC ta yi a dalilin wani rahoto da ta fitar a Nuwamban 2021.

Vanguard tace EFCC tayi wa wannan rahoto da ta fitar a shafinta na Facebook kwanaki take da ‘Hidden N19.3 billion Kogi salary bailout funds returned to CBN’.

Gwamnatin Kogi ta karyata zargin da ake yi mata na boye kudi a banki, ta ce har yanzu abin take da shi a asusu bai kai N20bn, duk da zargin an boye biliyoyin.

Ba a nan kawai EFCC ta tsaya ba

Bugu da kari, gwamnatin Kogi ta roki kotu ta tursasawa EFCC ta yadda za ta fitar da sakon neman afuwa nan da kwanaki biyu domin ta bada hakuri a gidajen jaridu.

Lauyoyin jahar ta Kogi su na so hukumar EFCC ta bada hakuri a kan irin rubuce-rubucen da ta rika yi, wanda a cewar gwamnatin jahar, soki-burutsu ne ba komai ba.

A ranar 17 ga watan Disamba, 2021, za a saurari wannan kara kamar yadda kotu ta bayyana.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here