Rundunar Sojoji ta yi Nasarar Kama Wani Hatsabibin Boka
Dakarun sojojin Najeriya sun yi nasarar kama bokan tsohon hatsabibin ɗan fashi Terwase Akwaza.
An kama Ugba Lorlumun mai shekaru 75 a duniya ne a kusa da matsafarsa da ke jihar Benue.
Sojojin sun ce sun kuma kama wasu daga cikin sauran ƴan kungiyar fashi da makamin na Gana.
Sojojin Najeriya na musamman da ke Doma a ƙaramar hukumar Doma na Jihar Nasarawa a ranar Laraba ta ce ta kama Ugba Lorlumun mai shekaru 75 da ake zargin bokan marigayi shugaban ƴan fashin Benue, Terwase Akwaza da aka fi sani da Gana ne, The Punch ta ruwaito.
An kuma kama Gana ne a Satumban 2020 sannan sojojin SF command da ke Doma suka kashe shi.
Read Also:
A yayin taron manema labarai a ranar Laraba, Kwandan 4 special forces, Manjo Janar Moundhey Ali ya ce an kama bokan tare da wani da ake kira ‘kwamanda’ a yayin da aka kai sumame wurin tsafin su.
Ya ce, “A Benue, mun kama babban bokan marigayi Terwase da aka fi sani da Gana da ɗaya daga cikin ƴan kungiyarsa da ake kira kwamanda sannan muka ƙona matsafar. Yayin da wani ɓata gari, Paul Duguma ya mutu a Katsina Aka.”
A hirar da ya yi da wakilin The Punch bayan sumamen, bokan ya ce, “Na yi wa mutanen Gana huɗu layyu, sun sake zuwa sun ce suna son layar zana sai na tambaya abinda za suyi da shi. Sun yi barazanar min duka sai na gudu zuwa gada inda sojojin suka kama ni.”
Kazalika, Ali ya kuma ce an kama karin wasu mambobin kungiyar marigayi Gana su 41.