AMNESTY: Sojin Najeriya Sun Kashe Mutum 38 Yayin Zanga-Zangar #EndSARS

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta ce sojojin Najeriya sun hallaka mutane 38 yayin zanga-zangar EndSARS ranar Talata.

Kungiyar ta ce bayanan da ta tattara sun tabbatar mata da cewa sojojin sun isa gurin da masu zanga-zanga suka taru a Lekki da misalin karfe 6:45 na yammacin ranar Talata, suka fara buɗe wa mutane wuta har zuwa karfe tara na dare.

Mutanen da suka rasa ransu a lamarin sun hada da ‘yan dabar da Amnesty ta ce ana zargin gwamnati ta ɗauko hayarsu don tarwatsa masu zanga-zanga, da ‘yan ba ruwana, da kuma masu zanga-zangar 12.

Hazalika Amnesty ta ce ta gano cewa an cire kyamarorin da aka tanada a wajen kafin ƙaddamar da wannan harin a kan mutanen da ta kira ”masu zanga-zangar lumana da ke neman gwamnati ta tashi tsaye don sauke nauyin da suka ɗora mata”.
”Buɗewa masu zanga-zangar lumana wuta babban laifi ne, na take hakkin jama’a, da ‘yancinsu na fadin albarkacin baki da damar da suke da ita ta shirya taron lumana, waɗannan sojoji manufar su guda daya ce tak, su kashe” in ji Osai Ojigho, daraktar kungiyar Amnesty International a Najeriya.

Kungiyar ta yi kira da a gudanar da sahihin bincike don zaƙulo mutanen da ke da hannu a kisan masu zanga-zangar, domin su girbi abin da suka shuka.

”Wannan kisa da alama kisan kiyashi ne, don haka akwai bukatar fara bincike na gaggawa,” in ji sanarwar da ƙungiyar ta aiko wa BBC.

Amnesty ta ce daga fara zanga-zangar zuwa yanzu, an hallaka mutum 56 zuwa yanzu, sannan ta yi imanin cewa jami’an tsaro sun yi amfani da ƙarfin da ya wuce ƙima wajen shawo kan zanga-zangar da ake yi

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here